June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ba dole sai dalibai sun nemi aikin gwamnati ba-kungiyar daliban Yusuf Maitama Sule

1 min read

Kungiyar dalibai wato Network For African Students Entrepreneur Yusuf Maitama Sule University Chapter ta ce daga
cikin ayyukan da kungiyar take gudanarwa shi ne bi yawa dalibai kudin Makaranta tare da koyar dasu Sana’o’in dogaro kai.

Shugaban kungiyar Kwamared Nuraddeen Rabiu ne ya bayyana haka a yayin da yake zantawa da jaridar bustandaily.

Nuraddeen ya kuma ce akwai dalibai da dama da kungiyar ta biya kudaden Makaranta domin tallafawa karatun su.

Haka zalika ya ce kungiyar takai dalibai gurare da dama domin koyon sana’o’i iri -iri.

Kwamarad Nuraddeen ya Kara da cewa kungiyar na kokarin kawar da hakidar nan ta ta’ammali da sha da fataucin miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai domin su dogara da sana’o’i.

Ya kuma bukaci matasa da nemi rancen bashi mara ruwa wanda babban bankin kasa na CBN zai Fara rabawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *