Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta buɗe babbar kasuwar jihar mai suna Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, bayan shafe fiye da watanni hudu kasuwannin jihar suna rufe.
1 min readGwamnan jihar Kadunan Malam Nasir El-Rufai dai ya ce an dauki
matakin rufe daukacin kasuwannin jihar ne don hana yaduwar cutar
Korona.
BBC ta ziyarci kasuwar da aka fi sani da Central Market da ke
kwaryar birnin Kaduna, wanda shi ne babban birnin jihar.
Kasuwar Sheikh Abubakar Mahmud Gumi ta kasance kasuwa mafi
girma a fadin jihar da dubban jama’a daga ciki da wajen jihar ke
kwararowa domin yin hada-hada.
Gwamnatin jihar ta ce ta yanke shawarar bude kasuwar bayan data
gamsu da matakan kariyar hana yaduwar cutar Korona wanda aka
dauka tsakanin gwamnatin da shugabannin ‘yan kasuwar.