July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kasuwar ‘yan kwallo: Makomar Thiago, Sancho, Chilwell, Oblak, Willian, Partey, Dybala, Havert

2 min read

Liverpool ta tuntubi Bayern Munich domin yiwuwar dauko dan wasan
Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (Bild, in German –
subscription required) .
Sai dai kuma, Liverpool ba ta son dauko dan wasan Vasco da Gama
dan kasar Brazil Talles Magno, duk da rahotannin da ke cewa dan
wasan mai shekara 18 zai tafi Anfield. (Standard)
Shugaban fannin kwallon kafa na Borussia Dortmund , Sebastian
Kehl, ya jaddada cewa dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon
Sancho zai ci gaba da zama a kungiyar duk da sha’awar da
Manchester United ke yi na dauko shi. (MEN)
United na shirin fafatawa da Chelsea a yunkurin dauko dan wasan
Leicester City dan kasar Ingila Ben Chilwell, mai shekara 23, a yayin
da Chelsea ta ce ba za ta iya biyan £80m kan dan wasan ba. (Mirror)
Golan Atletico Madrid dan kasar Slovenia mai shekara 27 Jan Oblak
zai yanke shawara kan makomarsa a yayin da aka ce Chelsea na
zawarcinsa. (AS)
Manchester United na son Dembele, Aston Villa na zawarcin
Watkins
Dan wasan Barcelona ya kamu da korona
A karshen makon nan Arsenal za ta sanar da dauko dan wasan Brazil
Willian, mai shekara 32, kan kwangilar shekara uku bayan zamansa
ya kare a Chelsea. (Telegraph – subscription required)
Arsenal za ta fuskanci kalubale daga Juventus a kokarinta na dauko
dan wasan Atletico Madrid mai shekara 27 dan kasar Ghana
Thomas Partey. (Gazzetta Dello Sport, via Mail)
Sabon kocin Juventus Andrea Pirlo ya gaya wa dan wasan Argentina
Gonzalo Higuain, mai shekara 32, da dan wasan Jamus Sami
Khedira, mai shekara 33, cewa za su iya yin gaba a bazarar nan.
(Goal)
Za a iya bayar da karin dama gaManchester United da Tottenham
domin sayendan wasan gaba na Argentina Paulo Dybala, mai
shekara 26, daga Juventus a bazarar nan. (Mirror)
United za ta bukaci Roma ta biya ta £20m kan dan wasan Ingila mai
shekara 30 Chris Smalling, wanda ya amince a rage albashinsa
domin ya tafi kungiyar da ke buga gasar Serie A. (Sun)
Napoli ta amince ta cimma yarjejeniya da Everton domin sayar da
dan wasan Brazil Allan, mai shekara 29. (Express)
West Ham tana son ta karbi fiye da £80m kan dan wasan Ingila
Declan Rice, mai shekara 21, a yayin da Chelsea take zawarcinsa
(Times – subscription required)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *