July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyoyin Addinai Sun Nemi Hanyar Shawo Kan Rikici a Jihar Kaduna

2 min read

Majalissar koli ta tabbatar da
shari’a reshen Kaduna ta ce mafita kawai ita ce
hukunta masu laifi da kuma taron sulhu tsakanin al-
umar yankin.
Majalissar da ta kira taron manema labaru don nuna
damuwa game da rashin zaman lafiya a kudancin
Kaduna ta ce matukar gwamnati ba za ta hukunta masu
laifi ba, to rikici ba zai kare ba.
A cikin hirar sa da Sashen Hausa, Malam Abdurrahman
Hassan, sakataren majalisar ta koli n
Ya bayyana cewa, gwamnati ta kakkafa kwamitoci a
lukutan baya da nufin neman hanyar shawo kan
matsalar sai dai rashin aiwatar da shawarwarin
kwamitin ne sanadin ci gaba da tashin hankali domin
ba a hukunta wadansu ba ya zama ishara ga masu
neman tada fitina.
A nata bangaren, kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato
CAN tana da ra’ayin cewa matsala ce ta cikin gida dake
bukatar al-umar yankin su zauna su tattauna. shugaban
kungiyar CAN a jahohi sha tara na Arewacin Najeriya
Reverend Yakubu Pam ya ce an jima ana fama da
rikicin sabili da haka al’ummar yankin ya kamata su
zauna su tattauna, su fahimci juna.
A da dai hare-haren ‘yan-bindiga sun addabi al-umar
yankunan Kerawa, Giwa, Birnin Gwari kawai a jahar
Kaduna kafin daga bisani kuma suka koma yankin
kudancin Kaduna inda aka hallaka mutane da kuma
jikkata wasu da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *