June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sama da yara 80 aka kashe watanni uku

1 min read


Ƙungiyar bayar da agaji ta Save the Children ta bayyana cewa ‘yan tada
ƙayar baya sun kashe sama da yara 80 tsakanin watan Afrilu zuwa Yuli
a Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Congo.
Ƙungiyar ta bayyana cewa wannan lamarin ya faru ne a lardin Ituri, inda
kuma wasu yaran aka ci zarafinsu ta hanyar lalata.
Ƙungiyar ta ce an kai hari ga kusan makarantu 60 da kuma asibitoci 17
tsakanin ɗan wannan lokacin.
Ƙungiyar ta ce yanayin da ake ciki a arewa maso gabashin Congo na
kara tabarɓarewa a kullum.
Hare-haren da ‘yan bindiga suka kai na baya bayan nan ya yi sanadin
sama da mutum 300,000 suka rabu da muhallansu.
Sai dai rundunar sojin ƙasar ta ce ta yi nasara kan kusan duka
sansanonin ‘yan tayar da ƙayar bayan da ke yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *