‘Yan sanda sun ceto yaron da aka kulle a gidansu shekara 7
1 min read
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce an samu nasarar ceto wani
matashi da aka tsare shi a cikin gidansu tsawon shekara bakwai ba
tare da ba shi damar fita ba.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Haruna Kiyawa, ya tabbatar
wa BBC hakan ne a ranar Juma’a da safe.
A ranar Alhamis da yamma ne bidiyon da ke nuna yadda aka kuɓutar
da yaron ya watsu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta da
muhawara a faɗin ƙasar.
A cikin bidiyon an ga yadda wasu mutane suka ɗauke shi suka saka
shi a cikin motar ‘yan sanda aka tafi da shi, yayin da wasu mutanen
ke tattauna wa da shi yana nuna alamun farin ciki.
Sannan ƙasusuwan jikinsa duk sun fito, abin da ke nuna alamun
yunwa da rashin lafiya.
Duk da dai zuwa yanzu ba a tabattar da yawan shekarunsa ba, amma
alamu sun nuna zai iya kai wa shekara 20 da haihuwa.
Wannan lamari na zuwa ne a ranar da ‘yan sanda suka gurfanar da
mahaifin yaron da aka ceto a Birnin Kebbi ranar Lahadi, wanda aka
zargi matan ubansa da ɗaure shi a turken dabbobi tsawon shekara
biyu.