July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Abubuwan Mamaki game da Tarihin Rayuwar Sheikh Jafar Mahmud Adam

3 min read

Haihuwa da fara neman ilmi
An haifi marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ne a garin Daura, a
farkon shekarun 1960s.

Marigayi Ja’afar ya fara karatunsa na allo a
gidansu a Daura, a wurin mijin yayarsa, Malam Haruna, wanda kuma
dan uwansu ne na jini.
Daga nan kuma sai aka mayar da shi wajen wani Malam Umaru a wani
gari “Koza” da ke Arewa da Daura a jihar Katsina.

Bayan sun zo Kano
ne tare da wannan malami a 1971 sai ya zauna a makarantar Malam
Abdullahi a cikin Fagge.

Dama can Sheikh Ja’afar ya riga ya fara haddar Alkur’ani maigirma,
wanda ya kammala a shekara ta 1978.
Bayan da Malamin ya haddace
Alkur’ani ne sai ya ga bukatar ya samu ilmin Boko don haka ya fara
karatun zamani a 1980.
Har wa yau, Malam Ja’afar ya shiga makarantar koyon Larabci ta
mutanen kasar Misra a cibiyar yada al’adun kasar Misra (Egyptian
Cultural Centre), sannan kuma ya shiga makarantar Boko ta manya
watau “Adult Evening Classes.


A 1983 ne Malamin ya kammala wadannan makarantu 2 na Boko da
Arabiya, wanda daga nan ya samu shiga shiga makarantar GATC Gwale
a 1984, har ya kammala a1988. Bayan shekara guda ne ya wuce
Jami’ar Musulunci ta Madina.

A wannan babbar jami’ar musulunci ta Madinah ne Malamin ya karanta
ilimin tafsiri da Ulumul Kur’an, wanda kuma ya kammala a shekara ta
1993.

A wancan lokaci ne aka soma jin tafsirin sa na Al-Qur’ani a cikin
Garin Maiduguri.

Bayan nan Sheikh Ja’afar ya sami damar kammala karatunsa na digiri
na biyu (Masters) a Jami’ar Musulunci ta Oundurman a kasar Sudan.

Kafin rasuwar Malamin, yayi nisa wajen karatunsa na PhD) a Jami’ar
Usman Danfodio ta Sokoto.
KU KARANTA: Takaitacen tarihin Marigayi Mai shari’a Mamman Nasir

2. Malaman Marigayi Jafar Mahmud Adam
Kamar yadda Malamin ya fada daga cikin malamansa na ilimin addinin
Musulunci, akwai malaminsa na farko, mutumin kasar Masar, Sheikh
Abdul-Aziz Ali al-Mustafa, da kuma Malam Nuhu a unguwar Dandago
da ke cikin Kano.

A wajen Malam Dandago ne Marigayin ya karanci ilimi fikihun malikiyya
da wadansu littattafai na hadisi.

Sauran Malaman sun hada da
Muhammad Shehu, mutumin Lokoja, wanda Malam ya karanci nahawu
da sarfu da balaga da adab.
Akwai kuma Sheikh Abubakar Jibrin limamin masallacin Juma’a na
BUK, akwai kuma Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim shi ma na jami’ar
Bayero ta Kano.

Har yanzu wannan babban Malami na Hadisi Ahmad
Ibrahim yana nan da ran sa.
Daga cikin malamansa na jami’a kuma, akwai Sheikh Abdurrafi’u da Dr.

Khalid Assabt da sauran su.
3. Karatu da darusan da Malam ya koyar a rayuwarsa
Daga cikin karatuttukan da malam ya karantar da su, sun hada da
tafsirin Alkur’ani mai girma. Ja’afar Adam ya sauke Al-Qur’ani kusan
sau 2 a Masallacin Muhammad Indimi da ke cikin Garin Maiduguri a
jihar Borno, a cikin shekaru barkatai.

Malam ya kuma karantar da Kitabuttauhiid na Sheikh Muhammad Ibn
Abdulwahab, da kuma littatafan hadisai na Umdatul Ahkaam, Arba’una
Hadiith.

Sauran darusa sun hada da wani littafin tauhidi da ya fice mai
suna Kashfusshubuhaat.
Haka kuma Malam ya karantar da litaffin nan na Bulugul Maraam,
Riyaadussalihiin, Siiratun Nabawiy, da kuma Ahkaamul Janaa’iz,
Siffatus Salaatun Nabiiy na Muhammad NasirudDeen Albany. 4. Almajirai
Wasu daga cikin daliban malam sun hada da Malam Rabi’u Umar R/
Lemo da Malam Sani Abdullahi Alhamidi Dorayi da Malam Abdullah
Usman Gadon Kaya da Malam Usman Sani Haruna da kuma Malam
Ibrahim Abdullahi Sani.
Sauran manyan Almajiran Marigayin sun hada da Malam Ali Yunus
Muhammad da Dr. Salisu Shehu da Malam Shehu Hamisu Kura da
kuma Malam Anas Muhammad Madabo.
Kafin rasuwarsa, Malam ya fara gagarumin aikin rubuce tafsirinsa a
harshen Hausa a karkashin wannan cibiya (Sheikh Ja’afar Islamic
Documentation Centre).
Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmoud Adam ya rasu ranar juma’a 26/
Rabii’u Awwal/1428 (daidai da 13/04/2007).

Malamin ya rasu ya bar
mata biyu, da ‘yaya shida, yayin da aka haifa masa ta bakwai kwanaki
58 daidai bayan an yi masa kisan gilla.

Dubun-dubatar mutane ne daga ko’ina cikin kasar nan suka halarci
jana’izarsa, kuma an binne shi ne a makabartar Dorayi. Allah ya ji kan
sa ya gafarta masa, ya saka masa da gidan Aljannatul-firdaus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *