September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Sojojin Najeriya sun tarwatsa ‘yan fashi a Kaduna.

1 min read
Sojojin Najeriya sun tarwatsa 'yan fashi a Kaduna.

Wani hari ta sama da rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kai ta sama ya
yi sanadiyyar halaka ‘yan fashi da dama a Dajin Kuduru da ke Jihar
Kaduna ta Arewaci maso Yammacin Najeriya.
A harin da ta kai ranar Alhamis, ‘yan fashin da ke da alaƙa da ƙungiyar
Ansaru ne da dama suka mutu bayan wasu bayanan sirri da rundunar
sojan ta samu, in ji hedikwatar tsaro ta Najeriya da ke Abuja.
Wani bidiyo da ta wallafa a shafukanta na zumunta ya nuna yadda aka
tarwatsa sansanin ‘yan fashin daga sama ƙarƙashin jagorancin wani
mai suna Mallam Abba.
Sai dai rundunar ba ta bayyana adadin waɗanda ta ce ta kashe ba ko
kuma rasa rai ko rauni daga ɓangaren dakarunta.
A tsakiyar wannan makon nan ne gwamnonin Najeriya suka yi wata
ganawa ta musamman game da matsalolin tsaro musamman a yankin
Arewa maso Gabas da kuma Yamma tare da Shugaba Muhammadu
Buhari.
Har wa yau, Kaduna na fama da rikice-rikicen ƙabilanci da na addini a
kudancin jihar, waɗanda da su ma suka jawo asarar rayukan mutane da
yawa. A makon da ya gabata sojoji suka ce sun kama mutum takwas
bisa alaƙa da rikicin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *