June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Jami’an tsaro za’a tuhuma kan matsalar batun tsaro-Masari

1 min read

Gwamnan jihar Katsina dake arewacin Najeriya Aminu
Bello Masari, ya zargi shugabannin rundunonin tsaron
kasar da gazawa wajen kawo karshen hare-haren ‘yan
bindiga a jihar. Yayin rabon baiwa mata dubu 1 da kuma dalibai 701 tallafi a karamar
hukumar Rimi, Gwamnan jihar ta Katsina ya ce abin mamaki ne da
takaici, zalika ya gaza fahimtar abinda ya sanya manyan hafsoshin
tsaron Najeriya gaza magance matsalar tsaron, duk da cewar
dukkaninsu ‘yan arewacin kasar ne, yankin da ‘yan bindigar suka
addaba, dan haka kamata yayi a caccaki hafsoshin tsaron amma ba
shugaban kasa Muhammadu Buhari ba.
Gwamna Masari ya kuma koka kan yadda yace a halin yanzu, ‘yan
bindigar na sajewa da mazauna kauyuka a jihar ta Katsina, abinda ke
zama karin barazana ga rayukan jama’a.
Ranar 10 ga watan Agustan da muke, ‘yan bindiga suka kai farmaki
karamar hukumar Kurfi, inda suka sace wata yarinya mai shekaru
13.
A baya dai gwamnan jihar ta Katsina ya yi kokarin cimma sulhu da
‘yan bindigar amma shirin ya gaza dorewa bayan saukin hare-haren
da aka samu na takaitaccen lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *