June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Makaman da jami’an tsaron Nigeria suke Amfani dasu tsofaffi ne

1 min read

Wani Rahoto da aka gabatar a Nigeria,yayi nuni da cewa makaman da jami’an tsaron Nigeria suke amfani dasu wajen yaki da ‘yan ta’adda da kuma mayakan bokoharam, sun yi tsufan da ke da bukatar a sabunta wasu.

A cewar Rahoton da Wata kungiya mai suna Action group for Good leaders ta fitar ta ce binciken ya nuna cewa makaman anyi amfani dasu ne sama da shekaru talatin baya.

Haka zalika rohoton ya kuma ce ‘yan ta’adda na amfani da makamai na zamani wanda sun fi karfin na jami’an tsaron Nigeria abinda ke zama babban kalubalan tsaro a kasar.

Nigeria dai na fama da rikicin boko haram da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *