July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Olympique Lyonnais ta doke Manchester City a gasar zakarun Turai 3-1

2 min read
Champion league

A yanzu haka babu wata kungiya daga kasar Ingila data rage a gasar.
Lyon wace ta kare a matsayi na bakwai a gasar league one ta kasar France,Wanda a yanzu haka kungiyoyi biyu ne daga kasar faransa da suka hadar Lyon da PSG.

Haka zalika a kasar Jamus ma kungiyoyi biyu ne suka rage wanda ya hadar da Bayern Munich kuma RBLifzing Wanda take a matsayi na uku a Bandasligar kasar jamus

Kungiyar kwallon kafa Liverpool Jurgen Klopp aka zaɓa gwarzon kocin gasar Premier
League a bana.
Kocin na Jamus mai shekara 53 shi ya taimaka wa Liverpool lashe
kofin gasar karon farko cikin shekaru 30.

Liverpool ta haɗa maki 99, inda ta lashe wasa 32 a wasanni 38,
tazarar maki 18 tsakaninta da Manchester City.

A Nigeria kuwa tsohon kyaftin din kungiyar Super eagles mai shekara 33, na dab da komawa kungiyar stoke city da taka leda.
Ana saran dan wasan zai sanya hannu a kan kwamtaragin shekara daya.

Dan wasan dai a yanxu bashi da kungiya tun bayan da ya bar kungiyar Trabzonspor dake Turkiya a watan Maris.

An kammala gasar cin kofin Unity Wanda ya gudana a karamar hukumar Rimin Gado.

Kungiyar kwallon kafa ta Bustan United ce ta lashe gasar bayan data doke kungiyar kwallon kafa ta Bilal Academy daci 3-1.

Kungiyar kwallon kafa ta Rimin Gado Shaning star ce ta zamo na uku a gasar bayan doke Golden bullet da ci 1- 0.

Da yake jawabi mashiryin gasar Alhaji Naseeb Ahmad ya ce sun shirya gasar ne domin hada kan matasa musamman ganin an kau da shaye- shayen miyagun kwayoyi a tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *