June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wani Liman a Kano ya kulle Dansa a gida shekara 15.

1 min read

Rundunar ‘ya sandan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta sake
ceto wani mutum da mahaifinsa ya tsare shi tswon shekara 15.
Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Kiyawa ya ce an tsare
Ibrahim Lawal ne mai shekara 33 tsawon shekara 15 a wani ɗaki.
Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda aka fitar
da mutumin daga wani ɗaki yana nishi jikinsa a ƙanjame. Jaridar intanet ta The Cable ta rawaito cewa mahaifinsa mai suna
Mallam Lawan limami ne a wani masallaci a birnin Kano.
Ya ƙara da cewa tuni aka kai mutumin asibiti sannan kuma sun fara
bincike game da lamarin.
Wannan na zuwa ne kwana uku kacal bayan ceto Ahmad Aminu –
wani mutumin da iyayensa suka tsare shi tsawon shekara uku .
Kazalika, a cikin makon da ya gabata ne aka kama iyayen wani yaro a
Jihar Kebbi bayan sun ɗaure shi a turken dabbobi na tsawon lokaci .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *