April 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yar shekara bakwai ta mallaki bindiga AK47 domin kare iyayenta

2 min read

Wata matashiya ‘yar Afghanistan ta samu yabo a kafafen sada
zumunta bisa gwanintar da ta nuna bayan yaƙar wasu ‘yan Taliban
biyu da suka kashe iyayenta.
Yarinyar ta yi amfani da bindigar gidansu ƙirar AK-47 wajen harbe
mutanen tare da raunata wasu da dama, a cewar jami’ai a Lardin
Ghor.
Jami’an sun ƙara da cewa ‘yan Taliban ɗin sun je gidan saboda
mahaifin yarinyar yana goyon bayan gwamnati.
Wani hoton yarinyar riƙe da bindiga dai ya karaɗe shafukan sada
zumunta a ‘yan kwanakin nan.
Daga baya kuma ƙarin mayaƙa sun sake dirar mikiya a gida da ke
ƙauyen Griwa amma kuma al’ummar yankin da mayaka masu samun
goyon bayan gwamnati suka fatattake su. Jami’ai sun ce tuni aka kai matashiyar da shekarunta ba su wuce
tsakanin 14 da 16 ba da ƙaninta wani waje domin kare su.
Ma’abota shafukan sada zumunta dai sun jinjinawa matashiyar.
“Mun jinjina mata saboda bajintar da ta yi”, kamar yadda kamfanin
dillancin labarai na AFP ya rawaito Najiba Rahmi na faɗa a shafin
Facebook.
“Mun san ba zai yiwu a maye gurbin iyaye ba amma martanin da kika
yi zai sa ki samu ɗan kwanciyar hankali,” a cewar Mohamed Saleh
shi ma a Facebook.
A cewar kafafen yaɗa labaran ƙasar, Ghor ɗaya ne daga cikin
Lardunan yammacin Afghanistan da ya fi fama da rashin ci gaba
sannan a lokuta da dama mata a yankin na fuskantar cin zarafi.
Ƙungiyar Taliban ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya
da Amurka a Fabrairu amma da dama daga mambobinta sun ci gaba
da neman a hamɓarar da gwamnatin Afghanistan mai ci da kuma
soke kundin tsarin mulkinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *