June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An kama wani Babban Mutum yana luwadi da yaro mai shekara 12

2 min read

Hukumar yaƙi da fasa-ƙwaurin bil’adama ta Najeriya (NAPTIP) ta ce
tana gudanar da bincike kan wani mutum bisa zargin aikata luwaɗi
da ƙananan yara har 12 a jihar Sokoto.
Ta yi iƙirarin cewa mutumin mai shekara talatin ya shafe kimanin
shekara biyar yana aikata wannan abu da ƙananan yaran kafin
dubunsa ta cika a ƙarshen mako.
Shugaban hukumar mai kula da jihohin Sokoto da Kebbi da Zamfara,
Mitika Mafa-Ali ya ce matashin ya riƙa bin shimfiɗar yaran ne cikin
dare a ƙauyen Rikina na ƙaramar hukumar Dange/Shuni.
Ya ce matuƙar bincikensu ya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya
aikata luwaɗi da yaran, ba shakka za su kai shi kotu tare da gurfanar
da shi gaban alƙali.
Mitika Mafa-Ali ya ce hukumarsu tuni ta gayyaci iyayen yaran da ake
zargi, mutumin ya aikata lalata da su, don karɓar bayanai daga gare. An kawo shi ne, domin ya koyar da yaran karatu. To ina jin iyayen ne
suka ba shi wuri, kuma a wurin kwana da shi da yaran, shi ne ya
samu wannan zarafi na yin lalatar, cewar Mista Mafa-Ali.
Ya ce duk da yake a fuska dai yaran na nan lafiya amma akwai
buƙatar kai su asibiti don gudanar da gwaje-gwaje, Saboda “irin
wa’yannan mutane in suna da HIV, yaran za su iya su kama”.
“To za mu yi ƙoƙari a nan ofishinmu, mu ga cewa yaran nan sun
samu cikakken lafiya, kafin mu gaya wa iyayen su tafi da su gida,” in
ji jami’in.
Bayanai sun ce tun farko, rundunar hizbah ce ta jihar Sakkwato ta
samu rahoton abin da ke faruwa kuma inda ta kama mutumin da
kuma tattaro yaran da ake zargin ya lalata.
Shekarun yaran daga takwas zuwa sha huɗu ne, wasu daga ciki yara
ne da ke halartar makarantar firamare, wasu kuma suna zuwa
makrantun islamiyya, kamar yadda Mafa-Ali ya shaida mana.
Jami’in ya ce mutumin da ake zargi ya bayyana wa ma’aikatansa
cewa ya aikata laifin, kuma a cewar wanda ake zargin abin da ya faru
aikin shaiɗan ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *