June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar DSS Ta Gayyaci Ghali Umar Na’abba

2 min read

Batun aika sammaci da hukumar
tsaro ta farin kaya wato DSS ke yawaita yi a duk
lokacin da wani dan Najeriya ya bayyana ra’ayinsa
game da muhimman abubuwa da suka shafi kasa ba
sabon abu ba ne kamar yadda rahotanni ke nunawa.
Na baya-bayan nan shi ne sammacin da hukumar ta
aika wa tsohon kakakin majalisar wakilan kasar, Ghali
Umar Na’abba da ke jagorantar wata kungiya mai
neman kawo sauyi da ake kira NC Front.
Shugaban kula da sha’anin jama’a na kungiyar ta NC
Front, Dr. Yunusa Tanka ya tabbatar da gayyatar da
aka yi wa Na’abba a shafinsa na Twitter a ranar
Lahadi.
The Nation is drifting to a police state!!! https://t.co/
PO4Mo2dTB8
— Dr Yunusa Tanko (@YunusaTanko) August 16, 2020
Rahotanni sun nuna cewa an aika masa da sammacin
ne bayan furucin da ya yi kan gazawar gwamnatin da
shugaba Buhari ke jagoranta tare da bayyana ajandar
kungiyarsa na NC Front ta kawo sauyi a kasar gabanin
zaben shekarar 2023.
Na’abba ya furta kalaman ne a wata hira da gidan
talbijin na Channels ya yi da shi.
A ranar Litinin hukumar ta DSS ta ke so Na’abba ya
bayyana.
Babban daraktan kungiyar fafutuka kare hakkin
fararen hula ta CISLAC kuma babban wakilin kungiyar
transparency international, Auwal Musa Rafsanjani, ya
ce suna wuce gona da iri tare da bata wa gwamnati
suna.
Rafsanjani ya kuma kara da cewa wadannan
hukumomin na kara bayyanawa al’umma cewa
gwamnati ba ta damu da su ba tare da jawo wa
gwamnati bakin jini.
Duk kokarin jin ta bakin hukumar DSS bayan tuntubar
hadimin hulda da jama’ar hukumar Peter Afunaya ya
cutura.
‘Yan Najeriya da dama dai na ci gaba da bayyana
rashin gamsuwar su da salon sammaci ko kuma
gayyatar da hukumar DSS ta dauka tun da shugaba
buhari ya dare kan karagar mulki.
A cikin makon da ya gabata ma hukumar DSS ta aika
sammaci ga tsohon mataimakin gwamnan babban
bankin Najeriya, Dakta Obadiah Mailafia a kan
furucinsa a yayin shirin gidan rediyon Nigeria Info
game da ayyukan ‘yan ta’adda.
Mailafia ya yi ikrarin cewa ya samu bayanan sirri daga
wasu tubabbun ‘yan Boko Haram cewa, daya daga cikin
gwamnonin arewacin Najeriya ke jagorantar kungiyar
Boko Haram lamarin da ya kai ga cin tarar gidan
rediyon na naira miliyan biyar, saboda zargin yada
kalaman ɓatanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *