Mutane 63 ne suka Mutu a yayin wata Ambaliyyar Ruwa
1 min read
Ƙasar Sudan ta ce mutum 63 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa
da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya haddasa tun daga watan
Yuli sannan guguwa ta raba dubbai da mahallansu.
Gidaje 14,000 ne suka rushe da kuma gine-gine 119, yayin da wasu
16,000 suka lalace, a cewar alƙaluman hukumar tsaro ta farar hula
wanda ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar.
Ana yawan samun ruwan sama mai yawan gaske tsakanin watan
Yuni zuwa Oktoba a Sudan sannan kuma a fuskanci ambaliyar a
kowacce shekara. Ofishin ayyukan jin ƙai na OCHA da ke Majalisar Ɗinkin Duniya ya
ƙiyasta cewa fiye da mutum 185,000 ne ambaliyar ta shafa sannan ta
ce akwai yiwuwar ci gaba samun ruwan saman a watanni masu
zuwa.
Jihohi 17 cikin 18 na ƙasar ambaliyar ta shafa, wadda ta haifar da
zaizayewar ƙasa.
“Ana ci gaba da buƙatar kayan tallafi a Sudan yayin da ƙasar ke fama
da bala’o’i daban-daban da suka haɗa da rikicin tattalin arziki da
ambaliya da annoba,” in ji OCHA.