June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tambuwal Ya nuna da muwarsa kan yadda matsalar tsaro ke muni a Sokoto

2 min read


Alamu na nuna cewa sai mahukumta sun yi da gaske kafin a
samu shawo kan matsalar rashin tsaro dake addabar
arewacin Najeriya musamman arewa maso yamma.
A daidai lokacin da aka samu
saukin matsalar rashin tasro a kananan hukumomin
Sabon Birni da Issa a gabashin Sokoto sai ga wata
matsala ta satar mutane don neman kudin fansa da
satar dabbobi a karamar mulkin Illela da kuma kisar
dauki dai dai a karamar hukuma ta Raba.
Karamar humukar Illela da take kan iyakar Najeriya da
Nijer, tana fuskantar matsalolin tsaro daban daban duk
da yake an girke jami’an tsaro da suka hada da na
hukumar hana fasa kwauri, sojoji, jami’an kula da
shige da ficen baki da ‘yan sanda da sauran su.
Matsalolin tsaro da ake fuskanta a wannan yankin sun
kuma hada da matsalar satar mutane da ta yi kamari a
yankin.
Bello Isa Ambarura, dan majalisa mai wakiltan yankin
a majalisar dokoki ta jihar Sokoto, ya ce gwamnatin
jihar da ta tarayya suna iya kokarin su domin tabbatar
da tsaro a yankin gabashin Sokoto, amma dai matsalar
satar mutane tana addabar yankin na Illela. Ya ce babu
rana da ba a samun labarin kai hari a kan mazauna
yanki.
Ambarura ya ce dole ne su koka domin a kawo musu
dauki a kan wannan batu, a don haka ya yi kira ga
gwamnati ta kawo ma yankin gudunmuwa don
al’ummar wurin su samu kwanciyar hankali.
Wadansu mazauna yankin da suka zanta da Muryar
Amurka a kan hali da suke ciki a yankin na gabashin
Sokoto sun bayyana cewa, mutanen yankin na bukatar
daukin gaggawa. Ya kuma ce mutane na jin tsoron
zuwa gona da wasu muhimman wurare domin gudun
kada a sace su a nemi kudin fansa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta ce tana sane da
abin da ke faruwa yankin kuma tana daukan matakan
magance wannan matsala, kamar yanda kakakin
rundunar ASP Mahamman ya shsidawa manema labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *