September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan gudun Hijira miliyan daya zasu koma garuruwansu-zulum

1 min read

Gwamnatin jihar ta gina sababbin
gidaje guda dari biyar a kauyen Ajiri da wasu rukunin
gidajen guda tamani a Auno a kananan hukumomin
Mapa da Konduga da samar da ruwan sha a wadannan
kauyuka da kayayyakin abinci ta kuma bada tallafin
Naira dubu hamsin hamsin ga kowane magidanci da
aka sake tsugunarwan.
Kwamishinan ma’ikatar gine gine da sake tsugunar da
jama’a Injiniya Mustpha Gubiyo, ya ce a yanzu haka
akwai mutane sama da dubu biyu da aka riga aka
tugunar da su a wadannan kauyuka kuma gwamnatin
ta tabbatar da an basu abubuwa da suke bukata na yau
da kullum. Ya ce gwamnatin jihar tana aikin hadin gwiwa da
ma’ikatar ministan noma domin raba musu gonaki su
fara aiki. Ya kuma bayyana cewa, gwamnati tana aiki
da sojoji da “Civilian JTF” da ‘yan sanda da kuma ‘yan
banga domin tabbatar da tsaro a kauyukan.
A cikin hira da Sashen Hausa, wadansu mazauna
kauyukan sun bayyana matukar jin dadin su da
wannan taimako da suka samu daga gwamnati. sun
kuma bayyana niyarsu ta ci gaba da gudanar hakokin
su na yau da kullum ba tare da tsoron ayyukan ‘yan
ta’adda ba, saboda yanzu babu batun Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *