June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gamayyar kungiyar Masoya Annabin Tsira ta bukaci Kisan Mai-Kano

1 min read

Gamayyar kungiyar masoya Annabi Muhammad Saw reshen jihar,Kano ta bukaci gwamnan jihar kano daya tabbatar an zartar da hukuncin kisa akan mutashinnan da yayi batanci akan ma’aikin tsira a nan Kano.

Shugaban Gamayyar Malam Shamsudden Salis ne ya bayyana haka,a yayin da yake zantawa da wakilin jaridar Bustandaily.
Ya ce da ana zartar da hukuncin kisa kamar yadda kotu ta zartarwa wannan matashi a baya-bayannan to da ansami raguwar aikata lamarin.

Shamsudden ya kuma karyata maganar da wasu ke cewa matashi mai yabon Annabi ne,inda ya ce ba mai yaban Annabi Muhd SAW,inda ya ce masoyin ma’aiki bazai aikata wannan mummunar hakida ba.
A satin daya gabata ne wata kotu a jihar Kano ta yankewa wani matashi hukuncin kisa kan batancin da yayi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *