September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Karota na karbar hudu 5000 a hannun mu a cewar masu babura mai kafa biyu-Kano

2 min read

Masu Babura mai kafa biyu, a Jihar Kano,sun bukaci gwamnati jihar Kano, data soke umarnin data bawa hukumar lura da zirga-zirgar ababan ta jihar Kano Karota, na kama masu a yayin da suka yi goyan biyu a Babura Mai kafa biyu.

A cewar mutanan korota na karbar kudade a hannunsu , a yayin da da suka kamasu.

Masu irin wannan abun hawa sun koka kan wannan mataki, inda suka ce bisa lalura suke goyon biyu, domin kuwa wasu daga cikin su na dauko ‘ya’yansu ne ko kuma matansu har ma da Iyayensu.

A cewarsu Jami’an KAROTA na karbar naira dubu biyar ko dubu uku a hannun su, inda wasunsu ke ganin cewa hukumar bata da wurimin kama masu babura saboda sunyi goyo.

Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar lura da zirga-zirgar abubuwan hawa ta Jihar Kano Karota, ya kuma yi mana yace tin lokacin tsohon gwamna Rabiu kwankwaso aka sanya dokar ,kuma a yayin aka dawo da dokar.

Kakakin na KAROTA ya kuma ce babu maganar cewa hukumar bata da hurimin kama masu baburan domin kuwa umarni ne daga gwamnatin Kano Kuma dole ne al’umma su bi wannan umarni.

Masu baburan dai na mika kokensu ga kungiyoyin kishin al’umma da ma hukumomin da abun ya shafa da su shigo musu cikin wannan al’amari, kasancewar suna cikin wani yanayi na rayuwa, yayinda ake fama da matsin tattalin arziki tun bayan bullar annobar Covid 19 a duniya baki daya.

2 thoughts on “Karota na karbar hudu 5000 a hannun mu a cewar masu babura mai kafa biyu-Kano

  1. A gaskiya yakamata Ku Lura sosai wajan yin rubutu, kuma yaxama dole wannan jarida mai albarka ta dinga yin editing kafin tai posting.
    Sannan tadinga amfani da alamar nan mai nuni da maganar da wanine yayita dan gudun canxa maganar da mutum yayi. Wato wannan ” a farko da Ku ma wannan ” a karshe. Akarshe kuma ina nuna gamsuwata da yadda kuke kokari wajan kawo labarai masu sahihanci. Allah yataimaki albustandaily da ma’aikatanta baki daya. Bissalam.

  2. Muna godiya sosai,kuma muna kokarin gyara matsalar.A gobe zamu nemi babban Editor Bilal Nasidi Muazu,wanda ke Kano domin jin yadda ake samun matsalar.

    Reporter dinsa suna rubutu batare da ya tace labarin ba,kawai kuma sai a gabatar da posting.
    Mlm Ibrahim Bustandaily nagodiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *