June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta ce Matashin da Mahaifinsa ya rufeshi shekara 15 yayi ne da niyyar Kisan kai

3 min read

‘Yan sandan jihar Kano sun ce sun shiga neman wani mutum mai
suna Malam Lawan Sheka, bisa zargin turke ɗansa tsawon shekara
15 cikin yanayin da bai dace da ɗan’adam ba.
Mai magana da yawun rundunar ya ce tuni kwamishinan ‘yan sandan
Kano ya ba da umarnin mayar da maganar hannun babban sashen
binciken laifuka na Bompai don faɗaɗa aikinsu.
DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi zargin cewa mahaifin Ibrahim
Lawan ya tsare shi ne da niyyar yi masa kisan mummuƙe.
“To bincikenmu ya nuna mana cewa ya kulle shi ne da niyyar ya
kashe shi. Saboda ya bar shi ba abinci, ba komai. Kuma gidanma ba
ma na mahaifinsa ba ne, na ita mahaifiyar matashin ne da ta rasu,” in
ji shi.
Ya ce har yanzu suna tsare da Binta Sulaiman, matar Malam Lawan
Sheka wadda “bayan auro ta (ne) suka ajiye shi cikin wannan
yanayi”. Baya ga matar, ‘yan sanda sun ce suna kuma yi wa mai unguwar
Sheka ta Kudu Malam Bello Da’u da wasu mazauna unguwar
tambayoyi kan wannan lamari.
Tun ran Lahadi ne ‘yan sanda suka yi awon gaba da mai ɗakin
mahaifin Ibrahim Lawal, don yi mata tambayoyi, sai dai wata
sanarwa da DSP Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ta
bayyana matar a matsayin ɗaya daga cikin wadda ake zargi..
Wani maƙwabcin gidansu matashin da ke unguwar Shekar Ɗan
Fulani a Kumbotso ya faɗa wa BBC cewa duk wani yunƙuri da
mahaifiyar Ibrahim Lawal ta yi a baya don kuɓutar da ɗanta, abin ya
ci tura.
Ya ce yayin kuɓutar da matashin, ‘yan sanda sun same shi a ɗaki
cikin mummunan yanayi, kuma ana zuba masa abinci cikin wani
babban kwano tamkar dabba. “Ko tafiya ba ya iya yi”.
Matashin dai shi ne na biyu cikin kwana biyu da ‘yan sanda suka
kuɓutar a irin wannan yanayi na turkewa a gida cikin yanayin da bai
dace da ɗan’adam ba.

Abdullahi Kiyawa ya ce sun ceto matashin ne a Sheka Unguwar
Fulani da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso bayan sun samu bayanai
daga jama’ar gari.
Ya ce suna ci gaba da bincike amma da zarar sun kammala za su
gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu gaban kotu.
Mai unguwar yankin, Malam Bello Da’u Sheka ya ce suna da
masaniyar cewa matashin kamar mahaifinsa, mahaddacin Ƙur’ani
ne, kuma akwai raɗe-raɗin cewa Ibrahim yana da taɓin hankali.
Ya ce a baya abokan Ibrahim Lawal sun taɓa yunƙurin tara
gudunmawa don kai shi asibiti, amma mahaifinsa ya ce yana nema
masa magani.
Basaraken ya ce ya shafe kimanin shekara takwas zuwa tara, bai sa
idonsa a kan matashin ba. “Ni da na ga ba na ganinsa, abin da na
ɗauka ko ubansa ya kai shi makaranta ta allo”.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Kano ya ƙara da cewa tuni suka
kai mutumin asibiti sannan kuma sun fara bincike game da lamarin.
‘Yan sanda dai ba su samu mahaifin Ibrahim Lawal a gida ba lokacin
da suka je kuɓutar da matashin ranar Lahadi.
Wannan na zuwa ne kwana uku kacal bayan ceto Ahmad Aminu –
wani mutumin da iyayensa suka tsare shi tsawon shekara uku .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *