June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zamu hada kai da hukumomi domin hana siyar da magunguna marasa inganci a Kano

2 min read

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, reshen jihar Kano ta ce Mutane Miliyan 14 ne,ke ta’ammali da kwayoyi a fadin Nigeria.

Kwamandan Hukumar a nan Kano, Dr “Ibrahim Abdul”ne ya bayyana haka,a yayin da kungiyar masu kananan shagunan siyar da magunguna ta jihar Kano,takaiwa hukumar ziyara da kuma hukumar Kula da Asbitoci ta jihar tare da hukumar kula da ingancin magagguna ta kasa
reshen Jihar Kano a yau.
Hukumar ta ce jihar Kano na fama da matsalar shan kwayoyi iri-iri, musamman ma a tsakanin matasa maza da mata.

Shugaban hukumar, ya ce duk da haka an sami saukin shaye-shayen kwayoyin kasancewar Kano ta dawo matsayi na shida a jerin jawoyin dake ta’ammali da miyagun akwayoyi.

Da yake nasa jawabin shugaban hukumar lura da ingancin magunguna ta kasa reshen jihar Kano Pharmacist, Sulaiman Chiroma,ya ce hukumar na fita ziyara duk sati domin sanya ido, kan masu shigo da magunguna Wanda suke gurbatattu.

Shi ma Pharmacist Ghali Sule Wanda shi ne Darakta a hukumar kula da Asbitoci ta jihar Kano, yayi kira ga kungiyar Masu kananan shagunan magani data kaucewa siyar da magunguna da hukumomi suka haramta siyarwa.

A nasa jawabin Sabon Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Nura Abubakar ya ce makasudun ziyarar shi ne saboda Kara neman hadin Kansu bisa irin kokarin da hukumomin suke gabatarwa a jihar.
Ya kuma bukaci yan kungiyar da basu sabunta Rijista dasu zo hanzarta yi kafin sati ya kare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *