June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Da hannun kishiyoyi ake tirke Yara a cikin gidaje.

4 min read

Wani ƙwararre kan fannin zamantakewa a Najeriya ya yi iƙirarin
cewa mafi yawa, kishiyoyi ne ke juya akalar mazan da kan ɗaure
‘ya’yansu tsawon shekaru a cikin gida ba tare da kyakkyawar kula
ba.
Dr. Usman Abdulƙadir na Jami’ar Usman Ɗan Fodiyo ya ce irin
waɗannan magidanta ba sa iya magana a lokacin da ake cutar da
‘ya’yan da suka tsugunna suka haifa.
A baya-bayan nan dai, sau uku hukumomi suna kuɓutar da wasu
yaran da iyayensu suka garƙame a gidaje cikin mummunan yanayin
da bai dace da ɗan’adam ba a jihohin Kano da Kebbi.
Ƙwararren ya ce yawancin yaran da kan shiga irin wannan tasku,
uwayensu ba sa gidan. Ya ce: “Ƙila, ko uwayen ba su nan, ko an
sallame su, ko kuma, ya zan ƙila yaron mahaifiyarshi ta rasu”.
A cewarsa abubuwan da ke faruwa ba yanzu suka fara ba. Irin
wannan ƙasƙanta ɗan’adam sun daɗe suna faruwa a ƙasar.

Dr. Usman ya ce ba hujja ba ce, uba ya tsare ɗansa tsawon shekaru
cikin irin wannan yanayi na ƙasƙanci, saboda batun rashin lafiyar
ƙwaƙwalwa. “Ai (su) ba asibiti ba ne,” in ji shi.
Ya ce da zarar an lura mutum yana da larurar ƙwaƙwalwa, to kamata
ya yi mahaifansa su garzaya da shi asibiti amma ba a yi tunanin
turke shi ba.
“Don ka ga yaron nan na Kebbi, duk yanayin rayuwarshi ya koma
kamar dabba, bai iya tafiya. Ga abubuwa nan da yawa. To,
wannan…ƙasƙanta ɗan’adam ne. Gaskiya, wannan bai zama dalili,”
cewar ƙwararren.
Masanin zamantakewar ya ce idan ma, ana tunanin kangara ce, yaro
ke fama da ita, to ai kamata ya yi a binciko sanadin da ya kawo
kangarar don magancewa.
Yawancin mazanmu da ke aure, wasu da yawan ba su isa yin aure
ba, Dr. Usman ya ce. “In ka ga kangara, yawanci ƙila uwayen sun
kasa rainon da Allah ya aza musu”.
Ya ce batun tufatarwa da makwanci da sauran buƙatun rayuwa gami
da matsin tattalin arziƙin da al’umma take ciki, duk suna da tasiri.
Bugu da ƙari ya taɓo kuma tasirin fina-finai da sauran baƙin al’adu
cikin sha’anin tarbiyya, waɗanda a cewarsa sun yi wa al’ummar
Hausa illa. “Kuma waɗannan, suna da tasiri kullum”.
Ƙwararren ya ce akasarin yaran da iyayensu suka tsare musu
buƙatun rayuwa, ba a cika ganin irin wannan kangara a tare da su.
Ba a nan gizo ke saƙar ba, in ji masanin. “Ai kana ganin yara da yawa
waɗanda uwayensu ke kula da su sosai, waɗanda suka samu
waɗanga abubuwa da aka sharɗanta na aure, da wuya ka ga sun
kangare.
Sannan akwai matsalar al’umma. Da, ka ga, ga al’ummarmu yaro na
kowa ne, amma yanzu kusan kowa ɗanshi ya sani.”
Dr. Usman Abdulƙadir ya ce su ma hukumomi suna da nasu alhaki
kan wannan matsala ta turke ‘ya’ya da wasu iyayen ke yi. Kamar
yadda wasu iyaye suka kasa da unguwanni, su ma hukumomi sun
kasa.
Matsalolin cin hanci da rashawa kan shafi gidaje
Ya koka kan yadda gwamnoni a yanzu ke yi wa tattalin arziƙin
ƙananan hukumomi ƙanshin mutuwa. “Idan kuɗin na yiwowa ƙasa ga
irin su ƙananan hukumomi, waɗanga ‘yan ƙananan abubuwa duk ana
iya riƙe su,” a cewarsa.
Ya kuma ce matsalolin cin hanci da rashawa a fannoni daban-daban
su ma suna da nasu tasiri cikin sha’anin tarbiyyar ‘ya’ya da riƙon
gida.
“Cin hanci da rashawa da yai yawa. Cikin harkar ilmi, cikin harkar
lahiya, cikin harkar noma. Za ka ga shi na ka sa, hash shi shigo cikin
gidajenmu a kasa zama lahiya,” masanin ya ce.
Dr. Usman Abdulƙadir ya ce daga cikin mafita kan wannan al’amari,
ya kamata ma’aurata su san manufar aurensu da kuma abin da ya
kamata su yi bayan sun samu yara.
Na biyu kuma, in ji shi. Dole sai mutane sun tashi tsaye. Duk
magidancin da ya kasa riƙe gidansa, to da wuya yaron nan ko yarinya
su zama na gari sai dai fa, idan Allah ya kare su.
Ƙwararren ya kuma ja hankali a kan komawa kan halayyar rayuwar
al’umma ta baya, lokacin da jama’a ke ganin cewa ‘kowa nawa ne’.
“Maƙwabcina, maƙwabcina ne, ɗa nai, ɗana ne. Ɗa na kowa ne.
Waɗanda ad da shi, su taimakawa waɗanda ba su da shi. Ba dole sai
ta hanyar kuɗi ba, ko ta hanyar tsawatar da yaro ne”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *