June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ecowas ta umarci sojojin Kasar Mali dasu bawa farar hula mulki.

1 min read

Ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka Ecowas ta yi tur da abin da ta kira
tawayen sojoji a Mali inda ta buƙaci sojoji su koma sansaninsu.
Wannan na zuwa ne bayan wasu harbe-harbe da aka yi cikin wani
sansanin sojoji da ke kusa da Bamako, babban birnin ƙasar.
Ecowas ta nanata rashin goyon bayanta ga duk wani yunƙurin sauyin
mulki ba bisa tsarin doka ba a yayin da soji suka kama shugaban kasar.
Tashin hankalin ya yi dai-dai da kiraye-kirayen zanga-zanga da ‘yan
hamayya ke yi ta neman Shugaba Ibrahim Boubkar Keita ta yi murabus.
Jama’ar ƙasar dai na nuna fushinsu kan aka samu taɓarɓarewar tsaro
da matsalar cin hanci da kuma rashin alkinta arzikin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *