Sojoji sun yi juyin mulki bayan kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta a kasar Mali
3 min read
Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keïta ya yi murabus daga mulki,
bayan sojoji sun tsare shi ranar Talata, kamar yadda gidan talbijin
ɗin ƙasar ya ruwaito
A wani jawabi ta aka yaɗa ta kafar talbijin, Ibrahim Keïta ya ce ya
kuma rusa gwamnatin ƙasar da majalisar dokoki.
Ya ƙara da cewa: “Ba na son a zubar da jini don ganin na ci gaba da
mulki”.
Al’amarin na zuwa ne bayan sojoji sun ɗauke su, shi da Fira Minista
Boubou Cissé zuwa wani sansanin soji da ke kusa da babban birnin
ƙasar Bamako, abin da ya janyo Allah-wadai daga ƙasashen yankin
da kuma Faransa.
Ana nuna fushi a tsakanin dakarun sojin ƙasar dangane da biyan
haƙƙoƙin aiki da kuma ka batun ƙazancewar faɗa da masu iƙirarin
jihadi – da kuma gagarumar rashin jituwa da tsohon shugaban ƙasar.
Shugaba Keïta ya lashe zaɓe wa’adi na biyu a shekara ta 2018, sai
dai al’umma na nuna fushi game da cin hanci da rashawa da kuma
rashin iya gudanar da harkokin tattalin arziƙi da ƙaruwar tarzomar
ƙabilanci a yankunan ƙasar.
Lamarin ya janyo manya-manyan zanga-zanga a karo da dama cikin
watannin baya-bayan nan.
Wani sabon ƙawancen ‘yan adawa ƙarƙashin jagorancin jagorar
addinin Musulunci, Mahmoud Dicko, ya yi kira a yi garambawul
bayan ya yi watsi da sassaucin da Ibrahim Keita ya yi wanda ya
haɗar da kafa wata gwamnatin haɗin kan ƙasa. Me muka sani game da boren sojoji?
Wani soja Kanal Malick Diaw – mataimakin kwamandan sansanin soji
na Kati – da kuma wani kwamanda Janar Sadio Camara ne ke
jagoranatar bore, Kamar yadda wakilin BBC Abdoul Ba a Bamako ya
ruwaito.
Bayan ƙwace sansanin ne, mai nisan kimanin kilomita 15 daga
Bamako, masu boren sun yi maci zuwa babban birnin, inda sowar
cincirindon mutane ta yi tarbe su.
Mutanen da suka taru sun buƙaci Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta
ya sauka daga mulki.
Lamarin ya faru ne jim kadan bayan kungiyar kasashen Yammacin
Afirka, Ecowas da kasar Faransa sun yi tir da harbe-harben da sojojin
suka yi a wani sansaninsu. Kakakin gwamnatin kasar Yaya Sangare ya tabbatar wa BBC Afrique
cewa an kama shugaban kasa da Fira minista.
Ibrahim Boubacar Keïta yana gidansa da ke Sebenikoro, Bamako,
lokacin da sojojin da suka yi tawaye suka kama shi da misalin karfe
4.30 na yamma a agogon kasar.
Yana tare da Firaiminista, Boubou Cissé, da dansa, da mataimakinsa
Karim Keïta.
Rahotanni sun ce ɗan shugaban ƙasar da shugaban Majalisar
Dokokin Mali da ministocin kuɗi da harkokin waje na daga cikin
sauran jami’an da sojoji suka tsare.
Ba a iya fayyace adadin sojojin da suka shiga cikin bore ba.
Sansanin soji na Kati ya taɓa jan hankula lokacin wani boren sojoji a
shekara ta 2012, bayan dakarun ƙasar sun yi fushi a kan gazawar
manyan kwamandojin Mali wajen dakatar da masu iƙirarin jihadi da
kuma Azbinawa ‘yan tawaye sun ƙwace iko da arewacin ƙasar.