June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan ci rani 40 sun mutu a hatsarin kwale-kwale-MDD

1 min read

Akalla ‘yan ci-rani 45 ne, ciki har da yara biyar suka mutu a wani
hatsarin kwale-kwale mafi muni da ya faru a wannan shekarar a
gaɓar tekun Libiya, in ji Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke
kula da ‘yan ci-rani.
Suna cikin mutum 80 da ke cikin wani kwale-kwale da injin ɗinsa
ya yi bindiga a gaɓar tekun Zwara, in ji hukumar.
Wasu mutum 37 da suka tsira ne suka bayar da rahoton haka. Su
ma waɗanda suka tsira ɗin wasu masu sana’ar kamun kifi suka
ceto su.
Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da ‘yan ci-rani da
kuma ƙungiyar kula da ‘yan ci rani ta duniya sun yi kira da a
matsa ƙaimi wurin ceto waɗanda hatsarin ya rutsa da su.
Sun bayyana cewa idan ba a dage wurin neman waɗanda suka yi
hatsarin ba, za a ƙara asarar wasu rayukan a tekun
Mediterranean.
Waɗanda suka tsira yawancinsu ‘yan Senegal ne, da Mali da
Chadi da Ghana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *