July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ecowas zata dauki mataki kan masu juyin mulki a Mali

3 min read

Shugabannin ƙasashen Afrika Ta Yamma za su yi wata tattaunawa
ta bidiyo kan juyin mulkin Mali a yau Alhamis.
Ƙungiyar Ecowas tana duba yiyuwa ƙaƙaba takunkumi kan waɗanda
suke da hannu a juyin mulkin da aka yi ranar Talata a ƙasar ta Mali.
Wani kanal ɗin soja Assimi Goita ya zama sabon shugaban mulkin
soja na ƙasar.
Faransa ta ce za ta ci gaba da ayyuakanta na soji kan masu da’awar
jihadi a Mali, duk da hamɓare tsohon shugaban ƙasar Ibrahim
Boubacar Keita. A ranar Alhamis ne kuma shugabannin sojin da suka yi juyin mulki
ranar Talata a Mali sun tattauna da shugabannin ‘yan hamayyar
kasar wadanda suka yi maraba da tumbuke gwamnatin Shugaba
Ibrahim Boubacar Keïta.
Sun dora masa alhakin gaza dakatar da hare-haren masu ikirarin
jihadi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin kasar a kansa.
Gamayyar ‘yan hamayyar ta ce ta yaba da kishin da sojin suka nuna
wajen son kafa gwamnatin rikon kwarya ta farar hula.
Wani Kanar na rundunar sojin kasar, Assimi Goita, shi ne ya zama
shugaban mulkin sojin.
Ya yi kira ga ma’aikata su koma bakin aiki.
Shugabannin ECOWAS za su yi taro yau
Shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma za su gudanar da
tattaunawa ta bidiyo kan rikicin Mali yau a birnin Niamey.
Taron na zuwa ne kwana guda bayan mataki cikin hanzari da
ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ta ɗauka a
kan Mali.
Ƙungiyar mai mambobin ƙasa 15 ta sanar da rufe kan iyakokinsu da
Mali da jingine duk wasu harkokin kuɗi da korarta daga hukumomin
zartar da al’amura.
Majalisar Ɗinkin Duniya ma ta bi sahun masu yin alla-wadai da juyin
mulkin sojiojin na Mali, da ya yi sanadin tilasta wa Shugaba Ibrahim
Boubacar Keïta sauka daga mulki.
Yayin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi
makamancin wannan kira na gaggauta sakin dukkan jami’an
gwamnati da kuma mayar da gwamnatin da tsarin mulki ya amince.
Ita ma Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali, tana cewa juyin mulki wani
abu ne tsohon yayi da ba za a sake lamuntarsa ba.
Sojojin da suka hamɓaras da gwamnatin Mali a wani juyin mulki sun
faɗa a jiya Laraba cewa babban abin da suka fi damuwa da shi, shi
ne tabbatar da zaman lafiya amma ba mulki ba.
Sun yi alƙawarin gudanar da sabbin saɓuka a wani abu da suka kira
cikin gwargwadon lokaci.
Sun zargi Shugaba Ibrahim Boubacar Keita da barin Mali ta
tsunduma cikin hargitsi da zaman kara-zube.
Ibrahim Boubacar Keïta ya lashe zaɓe a wa’adi na biyu cikin 2018,
sai dai tun daga watan Yuni yake fuskantar gagarumar zanga-zanga
a kan tituna dangane da cin hanci da rashin iya gudanar da tattalin
arziƙi da kuma taƙaddama kan zaɓukan majalisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *