July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Majalisar Dokokin Jihar Kano,ta aike da Sakon Murnar Sabuwar Shekarar Musulunci.

1 min read

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci al’ummar musulmin kasar nan da su kasance masu addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban kasa da kuma karuwar arziki a wannan lokaci da aka shiga sabuwar shekarar Musulunci.
Shugaban majalisar Alhaji Abdulazeez Gafasa ne ya bayyana hakan ta cikin sakon murnar shiga sabuwar shekarar musulunci da ya fitar fitr mai dauke da sa hannun jami’in yada labaran majalisar, Alhaji Ali Bala Kofar-kudu.
Shugaban majalisar ya kuma yi addu’ar fatan daukin ubangiji sakamakon matsalar tattalin arziki da al’umma suka tsinci kansu a ciki sakamakon cutar COVID-19.
Alhaji Abdulazeez Garba Gafasa, ya kuma ja hankalin mutane da su kasance masu tsoron All… a al’amuran su na yau da kullum tare da rungumar zaman lafiya kamar yadda addinin Islama ya koyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *