June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malamai na taimawa cin hanci da rashawa a Nigeria

1 min read

Majalisar koli kan harkokin addinin musulunci ta kasa ta zargi shugabannin addinai da tallafawa ayyukan cin hanci da rashawa sakamakon yin biris da suke yi da kuma nuna halin ko in kula kan annobar da ke zagon kasa ga ci gaban kasar nan.

Mataimakin sakatare janar na kungiyar farfesa Salisu Shehu ne ya bayyana haka yayin wani taro da shugabannin addinai da ke jihohin arewa maso yammacin kasar nan kan yadda za a dakile cin hanci da rashawa wanda ya gudana anan Kano.

Ya ce, kamata yayi shugabannin addinai su rika yawan yin wa’azi kan illar da cin hanci da rashawa ke da shi da kuma irin hukuncin da ubangiji zai yi ga mai aikata cin hancin.

Farfesa Salisu Shehu ya ce, fitowa karara a kalubalanci dabi’ar cin hanci da rashawa ba yana nufin yin fito na fito da hukumomi bane, amma lamari ne da ya zama wajibi shugabannin addinai su rika nuna kyamarsu akansa karara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *