July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matasa uku sun yi wa Yarinya mai shekaru uku Fyade-Katsina

1 min read

Lamarin dai a faru ne a garin Dan
Musa dake jihar Katsina, inda matasan uku masu
shekaru 13 zuwa 16 suka yi wa yarinyar mai shekaru
13 fyade, daga bisani suka kasheta suka jefa gawarta
cikin kogi.
Tun farko dai matasan uku da suka hada da Mubarak
Lawan da Anas Ibrahim da kuma Aliyu Mika, suna aiki
a gonarsu dake garin Dan Musa, suka hango ‘yan mata
da zarga da yi musu satar leman tsami.
Bayan da suka tunkari ‘yan matan ne sai suka gudu
suka bar yarinyar mai suna Safiya Basiru a baya,
matasan sun rike ta tare da cire mata kaya, sannan
dukkanninsu su ka kwanta da ita daya bayan daya.
Daga karshe yarinyar na ta faman ihu sai Aliyu Mika ya
dauki Yashi ya cika ma ta baki domin ta yi shiru. Bayan
ya kashe ta ya jefa gawar cikin kogi.
Domin sauraren hirar da Muryar Amurka ta yi da
matasan, saurari rahotan Sani Shuaibu Malumfashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *