July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Menene matsayin murnar Sabuwar Shekarar Musulunci

4 min read

A yau ne dai 1 ga watan Muharram 1442 bayan hijrar Annabi
Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madina.
Jama’ar Musulmi, batun Hijirah ba ƙaramin al’amari ba ne a wurin
al’ummar Annabi Muhammad (SAW). Don haka ya zama wajibi a kan
duk Musulmai su dauke shi da matukar muhimmanci.
Kamar yadda kuka sani, a duk lokacin da muka doshi shiga sabuwar
shekarar Musulunci ta hijirah, to za mu ga ana yawaita tattauna
maganganu muhimmai a kan ta, wani lokaci kuma a yi ta hayaniya.
Daga cikin abubuwan da ake yawan tattaunawa a kai cikin irin
wadannan lokuta da ake fuskantar shigowar sabuwar shekarar
Musulunci, akwai hukuncin yin bukukuwan sabuwar shekara. Shin ya
halatta ko bai halatta ba? Shin bidi’ah ne ko Sunnah ne?
A gaskiya cikin abun da na karanta, kuma na fahimta shi ne, wannan
mas’ala ce da magabata na can baya sosai ba su tattauna a kan ta
ba, (ma’ana) wata tattaunawa ta musamman. Sai dai Malaman da
suka zo daga baya-bayansu, su ne suka tattauna a kan ta. Misali:
Imam As-Suyudi – Allah ya jikan sa da rahama – ya ambace ta a cikin
littafinsa mai suna: ” ﻭﺻﻮﻝ ﺍﻷﻣﺎﻧﻲ ﺑﺄﺻﻮﻝ ﺍﻟﺘﻬﺎﻧﻲ ” a cikin juzu’i na daya,
da ke cikin littafinsa ” ﺍﻟﺤﺎﻭﻱ ﻟﻠﻔﺘﺎﻭﻱ “, ga abin da yace:
“Imam Al-qamuli ya ce, ban ga mutanenmu (ma’ana mazhabin
Shafi’iyyah) sun yi wata magana ba a kan taya murnar Idi, ko
shekaru, ko watanni, kamar yadda mutane suke yi ba.
Amma na gani a cikin fa’idodin da aka cirato daga Zakiyyuddini
Abdul’azim Al-munziri, cewa lallai babban malami Abul-Hasan Al-
makdisi an tambaye shi game da taya murna a farkon shigar
watanni, da shekaru, shin Sunnah ne ko bidi’ah? Sai ya bada amsa
kamar haka:
“Mutane ba su gushe ba suna sabani a kan haka, sai dai ni ina ganin
halal ne kawai, ba Sunnah ba ne ba bidi’ah ba. Haka ma Sharaf –
Algazzi ya cirato a cikin sharhin littafin Al-minhaj, kuma bai kara
komai a kai ba.” [Duba Al-Hawi, Juzu’i na 1, shafi na 82]
Haka an ruwaito Imam Ahmad – Allah ya jikansa da rahama – yana
cewa a game da taya murnar idi ma, ba sabuwar shekara ba:
“Ni ba na fara taya wani murnar idi, amma idan wani ya fara min, to
ina mayar masa.”
Sai Shaikhul Islam Ibn Taymiyyah, Allah ya jikansa da rahamarsa, ya
ce:
“Imam Ahmad ya yi haka ne saboda mayar da gaisuwa tilas ne,
amma fara taya murna ba Sunnah ce da aka yi umurni da ita ba,
sannan kuma ba a hana yi ba, wanda ya aikata ya yi koyi, wanda
kuma ya ki ya yi, shi ma ya yi koyi.”
A karkashin haka, ina iya cewa: taya murnar shiga sabuwar shekarar
Musulunci, halal ne a wurin wasu malamai, wanda ba ya da alaka da
ibadah, wato al’ada ce ta mutane su taya junansu murna ba don
suna tsammanin wata lada daga wurin Allah ba.
A wurin wasu malamai kuwa ba a yi, kuma suna ganin cewa bidi’ah
ce, matukar an alakanta shi da addini, wato idan mutane suna ganin
cewa abun da suke yi wani abu ne da addini ya yi umurni da a yi shi.
Wadannan Malamai, kuma suna kafa dalili da cewa, magabata ba su
yi ba.
Sannan kamar yadda ya zo a tarihance, Imam Hafizul Maqrizi ya ba
da labari a cikin littafinsa mai suna “Al-khutat” cewa:
“Sarakunan gwamnatin Ubaidiyyah ta ‘yan Shi’a a Misrah, su ne suka
fara gudanar da bikin sabuwar shekara.”
Sannan daga cikin abun da ya kamata mu lura da shi a nan shi ne, a
Musulunci, bayan ranakun Sallah karama da Sallah babba, ba wata
rana a shekara da aka umurci Musulmi su yi riko da ita a matsayin
ranar bikin shekara.
Duk da yake akwai wasu ranaku masu tarihi a Musulunci, irin ranar
hijirah, ranar yakin badar, ranar sulhun hudaibiyyah, ranar fathu
Makkah da sauransu, amma Musulmin farko ba su yin bikin tunawa
da daya daga cikin wadannan ranakun ko wasunsu.
A karkashin haka ne Malamai da dama suka ba da fatawa a kan
cewa bikin murnar sabuwar shekarar Musulunci bidi’ah ne, ba shi da
asali a cikin addinin Allah, don haka wajibi ne ga Musulmi su bar shi.
Sannan wani karin abun da ya kamata mu fahimta a nan shi ne, cewa
halal ne taya murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci a wurin
wasu malamai, ba yana nufin halatta taya wadanda ba musulmi ba
murnar shiga sabuwar shekararsu ta miladiyyah, kamar yadda Imam
Ibnul-Qayyim yayi bayani a cikin littafinsa mai suna, ” ﺃﺣﻜﺎﻡ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺬﻣﺔ “, a
inda yake cewa:
“Amma taya murna da abubuwan alamomin kafirci, wadanda suka
kebanta da shi, haramun ne, babu sabani a kan haka tsakanin
malamai. Kamar mutum yace: barka da idi, ko makamancin haka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *