Za’a bude Makarantun Nigeria a watan Satumba 2020
1 min read
Wasu jaridun Nigeria sun ruwaito cewa tini tattaunawa tayi nisa tsakanin Gwamnatin tarayya da kuma kwamitin karta kwana mai Yaki da annobar covid 19.
Haka zalika Wata jarida a Nigeria ta wallafa a shafinta na Instagram da facebook cewa Mininstan Ilimi Adamu Adamu ya zanta da Shugaban hukumar Kula da Jami’o’in Nigeria,kan bude Makarantun.
Rahoton ya nuna cewa a Ranar 7 Ga watan Satumbar Shekarar da muke ciki ne, za’a bude Makarantun.
Idan dai za’a iya tunawa kungiyar malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta tsunduma yajin aiki gabanin bullar annobar Covid 19.