July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar Lauyoyi ta bukaci Gwamnan Kaduna ya gurfana a gabanta

1 min read

Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Gwamnan jihar
Kaduna Nasir El-Rufai, biyo bayan zanga-zangar da wasu lauyoyi suka
yi kan gayyatar.
A wani saƙo da Ƙungiyar Lauyoyin ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce
ta yanke shawarar janye goron gayyatar da tura wa gwamnan kuma tuni
ta shaida wa gwamnan matakin da ta ɗauka.
Tun da farko dai wani lauya ne mai suna Usani Odum ya ƙaddamar da
takardar koke ta intanet inda ya nemi ƙungiyar ta janye gayyatar da ta yi
wa gwamnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *