Labari da dumi duminsa-An harbe dogarai shiga
1 min read
An harbe dogarai shida na Mataimakin Shugaban Sudan Ta Kudu,
James Wani Igga, bayan an kai hari ga ayarin motocinsa.
Mai magana da yawunsa, Kalisto Lado, ya shaida wa bustandaily cewa wasu
‘yan tawaye ne suka kai harin inda kuma suka raunata mutum biyu
bayan shidan da suka kashe.
Mista Wani ba ya cikin jerin ayarin motocin da aka kai wa harin a
mahaifarsa da ke ƙauyen Lobnok, kudu da babban birnin ƙasar Juba.
Harin wanda da aka kai a ranar Laraba ya faru ne yayin da ‘yan tawaye
daga ƙungiyar National Salvation Front suka tare motar da dogaran
suke ciki suka lalata ta kuma suka ƙona motar.
Har yanzu dai ƙungiyar ba ta ce komai ba kan wannan harin.
Mista Igga na cikin mataimakan shugaban ƙasa biyar da ake da su a
Sudan Ta Kudu, kuma shi ke kula da harkokin tattalin arziƙin ƙasa