Yajin aikin masu gura a Kano ya haddasa tsadar gurasar a yau
1 min read
A jiya ne dai kungiyar masu siyar da gurasa a jihar kano ta sanar da fara yajin aikin, a sakamakon tsadar fulawa da kara wanda shi ne makamashin gurasar.
A yau juma’a gurasar tayi karanci a nan kano,inda matasa da dama suka koka,kan matakin da masu gurasar suka dauka.
Matasan dai sun bukaci ‘yan kasuwa da gwamnati dasu saukakawa al’umma musamman a wannan yanayi na annobar covid 19.
Masu gurasar sun ce,ko a yau juma’a shagunan dake siyar da fulawa a kano, babu fulawar sakamakon tsada da fulawar tayi.