July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan gudun hijira na shiga kungiyar – Gwamna Zulum

3 min read

Gwamnan jihar Borno da ke Najeriya, Babagana Zulum, ya shaida wa
BBC Hausa cewa kungiyar Boko Haram tana ci gaba da daukar
mutane domin su taya ta yaki.
“Gaskiya ne kungiyar Boko Haram na ribatar mutane domin su shiga
cikinta kuma hakan kuma abin tsaro ne,” in ji gwamnan.
Sai dai Gwamna Zulum ya tabbatar da cewa “idan har jama’ar da ke
sansanonin ‘yan gudun hijra a jihar Borno ba su samu abin da suke
so ba musamman damar komawa garuruwansu domin noma to fa
dole ne su shiga kungiyar Boko Haram.
“Mutane sun gaji da zama a sansanin masu hijra. Ba sa samun abin
da suke so. Dole ne su koma garuruwansu domin samun damar yin
noma da kiwo kasancewar babu wata gwamnati da za ta iya samar
da ciyarwa gare su mai dorewa,” a cewar Gwamna Zulum.
Dangane da garuruwan da jama’arsu suka koma, Farfesa Babagana
Umara ya ce sun samu nasarar mayar da mutane garuruwansu
kamar Kukawa da Mafa sannan nan ba da jimawa ba “za mu mayar
da mutanen Kawuri.”
“Amma muna fatan sojoji za su kara kaimi wajen ganin an mayar da
al’ummar Baga da Marte da Malam Fatori da Guzamala”. Gwamnan jihar ta Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a wata hira
ta musamman da sashen Hausa na BBC, ya ce yanayin tsaro a jihar
tasa na bunkasa amma har yanzu akwai sauran rina a kaba
kasancewar Boko Haram na maboyarsu.
Ya ce: “‘Yan kungiyar na fakewa a tafkin Chadi da kuma dajin
Sambisa. Kuma idan har ba a bi su har ciki ba an kore su ba to fa
akwai matsala. Korar su daga hedikwatarsu ita ce hanya guda daya
ta kawo karshen Boko Haram.”
Sai dai kuma gwamnan ya ce shiga tafkin Chadi da Zambisa dole ne
sai Najeriya ta samu hadin kai na gaskiya da kasashen tafkin na
Chadi.
Boko Haram: Zulum ya ce jami’an tsaro na yin zagon ƙasa a
yunƙurin kawar da ƙungiyar
Kun san direban tasi da ya zama gwamnan Borno?
Dangane da tambayar da aka yi wa Gwamna Zulum ko akwai wasu
wurare da kungiyar Boko Haram ke rike da su a jihar ta Borno? Sai
gwamna ya ce ” gaskiya fisabilillahi babu wani yanki da ke hannun
kungiyar Boko Haram, sai akwai yankunan da babu jama’a a cikinsu.
Abin da nake nufi shi ne har yanzu jama’a ba su koma garuruwansu
ba.”
Ya kara da cewa “wallahi kafin zuwan Shugaba Buhari yanayin tsaro
a jihar Borno ya yi muni kwarai saboda a lokacin kananan hukumomi
20 ne a karkashin Boko Haram amma yanzu ba haka ba ne.”
Yaushe za a kare Boko Haram?
Akwai dubban jama’a da ke sansanonin daban-daban a jihar Borno
Da aka yi wa gwamna Babagana Zulum wannan tambaya, sai ya ce ”
hanya daya ta kawo karshen Boko Haram ita ce tabbatar da alaka mai
kyau tsakanin sojoji da farar hula.”
Ya kara da cewa “na sha magana cewa duk inda ka je za ka ga sojoji
da ‘yan banga tare. Amma abin da nake cewa shi ne sojoji su bai wa
farar hula kariya domin samun damar komawa gidajensu su yi
noma.”
Farfesa Zulum ya kuma ce tabbas sojoji na iya bakin kokarinsu
amma abin da ya “dame mu shi ne yaushe ne wannan yaki na Boko
Haram zai kare.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *