July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yanzu-yanzu Mutane Biyar suka Mutu a wani Sabon rikici

1 min read

Jami’ai a ƙasar Habasha sun bayyana cewa akalla mutum biyar aka
kashe yayin wata arangama tsakanin jami’an tsaron ƙasar da masu
zanga-zangar neman sakin shugabannin ƙabilar Oromo da aka kama.
Ƙungiyoyin kare haƙƙi sun bayyana cewa adadin waɗanda ke mutuwa
na ƙaruwa sosai.
Rahotanni a ƙasar sun ce an kashe mutane a wurare da dama.
Zanga-zangar ta ɓarke ne a ranar Talata bayan wani gangami da aka yi
a shafukan sada zumunta inda ake kira da a saki shugabannin ‘yan
adawa a ƙasar, Jawar Mohammed da kuma Bekele Gerba.
An kama su ne tun a watan Yuni bayan da aka harbe shahararren
mawaƙin nan ɗan ƙabilar Oromo Hachalu Hundessa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *