September 21, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Alummar Mariri dake jihar Kano sun zargi mijin wata mata Mai juna Biyu da laifin kulleta a gidan har ta rasa ranta

1 min read

Al’ummar maririn a jihar sun ce, matar ta dauki tsahon lokaci da mutuwa wanda har taikai gawar matar, ta fara tsutsa da wari, a sakamakon mutuwar matar tsahon lokaci.

Sai dai wasu mutune da jaridar Bustandaily ta zanta dasu sun bayyana cewa mijin matar ne, ya kashe domin kuwa a baya matar sun sha samun sabani da mijin nata.

Haka zalika wata mata wacce makociyar marigayiyar ce ta ce, matar tana dauke da juna biyu ne kuma ta taba shaidawa mata cewa, mijinta ya baya son ta haife masa juna biyun da take dauke dashi.

Rundanar ‘yan sandan jihar Kano a ta bakin kakakin rundunar sandan, DSP Abdullahi Haruna kiyawa, “ya ce rundanar tana ci gaba da bincike kan lamarin.
A baya-bayan sai an sami iyayen da suka daure ‘yayansu a nan Kano tsahon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *