Labari da dumi duminsa-Yan bindiga sun kashe ɗan sanda
1 min read
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani kurtun ɗan sanda a ofishin ‘yan
sanda na Ikolaba da ke birnin Ibadan na Jihar Oyo, a cewar rahoton
kamfanin dillancin labarai na NAN .
Lamarin ya faru ne ranar Juma’a yayin da maharan da ba a san ko su
wane ne ba suka buɗe wuta a kan ofishin bayan sun shiga cikin
farfajiyar ginin.
Kazalika, ba a san dalilin kai harin ba har zuwa da NAN yake haɗa
wannan rahoton.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Olugbenga Fadeyi
ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya ce suna kan bincike.
“Yanzun nan muka samu labarin harin amma ban samu ƙarin bayani ba
game da ɗan sandan da aka ce an kashe,” in ji shi.
“Mun tura jami’an tsaro yankin kuma da zarar mun samu ƙarin bayani
za mu sanar da ku.”