July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Masu zanga-zanga sun cinnawa ofishin majalisa wuta.

1 min read

Masu zanga-zanga a lardin Basra da ke Iraƙi sun yi arangama da
jami’an tsaron ƙasar, inda suka cinna wa wani ofishin majalisa wuta.
Jami’an tsaron sun harba bindiga a sama domin tarwatsa masu zanga-
zangar inda suke buƙatar gwamnan lardin na Basra ya yi murabus.
Hakan na zuwa ne bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba
suka harbe wasu ‘yan gwagwarmaya a wasu hare-hare da suka kai a
kwanakin baya.
Firaiministan Iraƙi Mustafa al-Kadhimi ya kori shugaban ‘yan sanda na
Basra da wasu jami’an tsaro a ranar Litinin inda ya bayar da umarnin
gudanar da bincike kan lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *