July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

‘Yan kasuwa na boye fulawa a kasuwanni

1 min read

Wani rahoto ya yi nuni da cewa, ‘yan kasuwa a nan Kano, na boye fulawa domin kara farashinta a kasuwanni.

A cewar wasu mutane,sun ce fulawar tayi karanci wanda sai an kai ruwa Rana ake samu,amma akwai fulawar, kawai an boye ne, da nufin kara farashinta.

Halima shitu, daya ce, daga cikin masu gudanar da sana’ar gurasa ta bayyanawa jaridar bustandaily cewa,tsadar fulawar ne, ya sanya gurasar tayi karanci a kano.

Ka zalika ta kara da cewa karancin fulawar ne ya sanya kungiyar tsunduma yajin aiki, domin fadakar da gwamnatin jihar kano, n irin abinda yan Kasuwa suke gudanarwa a yanayin annobar covid 19.

Gurasa dai na daya daga cikin abinci da hausawa ke amfani da ita tsahon lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *