July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

INEC ta fitar da jadawalin karshe na zaben cike gurbi

1 min read

Hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC ta fitar da jadawalin
karshe na yadda zaben cike gurbi na gwamnan jihar Ondo zai
kasance a ranar 10 ga watan Octoban shekarar da muke ciki.
Hakan na cikin wata sanarwa da jami’in wayar da kai na hukumar
zabe ta kasa INEC Festus Okoye ya fitar a Abuja.
Okoye ta cikin sanarwar ya bayyana cewa jadawalin wanda hukumar
ta INEC ta aike da shi zuwa kananan hukumomin da ke jihar ta Ondo
kuma za a iya samun jadawalin a Website din hukumar.
Sanarwar ta bayyan cewa hukumar ta sanya ranar 18 ga watan
Agusta ya zamo ranar da za a kammala karbar takardun sunayen
yan takara a kowacce jiha sai dai har kawo yanzu jam’iyyu hudu ne
kacal suka mika da takardar sunayen ‘yan takarar ta su.
Ta cikin sanarwar dai, Okoye ya ce hukumar a zamanta na ranar
alhamis ta yanke hukuncin fara gabatar da zaben gwamnan jihar
Ondo da kuma sauran zabubbukan cike gurbi da za gudanar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *