September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mai dakin shugaban Kasar Nigeria Aisha Buhari ta magantu bisa matsalar data samu a jiya

2 min read

Mai ɗakin shugaban Najeriya Aisha Buhari ta ce jirgin da ya ɗauko
ta domin dawo da ita gida daga jinyar da ta yi ya fuskanci matsala.
Sai dai ta ce matuƙa jirgin da ma’aikatansa sun nuna ƙwarewa da
bajinta wurin sassaita shi.
Ta bayyana haka ne a saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter bayan
komawar ta Najeriya daga jinyar da ta kwashe lokaci tana yi a ƙasar
waje.
“Zan yi jinjina da kuma nuna jin daɗina game da jajircewa da
ƙwarewa da direban jirgin da ma’aikatansa suka nuna, da kuma
zaratan sojojin sama maza da mata na rundunar sojin sama na
Najeriya kan aiki tuƙuru da suke yi wurin kula da jiragen rundunar,” in
ji ta. Aisha Buharin dai ta bar Najeriya ne tun bayan Babbar Sallah inda
wasu jaridun Najeriya suka ruwaito cewa ta tafi Haɗaɗɗiyar Daular
Larabawa domin neman magani.
Sai dai ko a saƙon da ta wallafa a shafinta na Twitter, sai da ta yi
hannunka mai sanda ga ɓangaren kiwon lafiya na Najeriya inda ta ce
ya kamata a ƙara inganta shi domin rage tafiye-tafiye zuwa ƙasashen
ƙetare domin neman magani.
Ko a shekarun baya sai dai uwar gidan shugaban ƙasar ta yi tir da
asibitin fadar shugaban ƙasar inda ta ce yana cikin wani hali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *