September 22, 2023

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Malaman islamiyya sun yi Alkunutu a Kano

1 min read

Kungiyar Alarammomi mahaddata Al’kur’ani ta kasa reshen jihar
Kano ta gudanar da Alkunutu a wani mataki na janyo hankalin
gwamnati don bai wa makarantun allo da islamiyya damar ci gaba da
karatu a jihar nan.
Shugaban kungiyar Alarammomi Malam Gwani Sunusi Abubakar ne
ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala sallar ta Alkunutu
wadda ta gudana a yau.
Malam Gwani Sunusi yace sun shirya yin Alkunutun ne da nufin
zaburar da gwamnati ta duba halin da ilimin addini ya shiga
sakamakon dakatar da makarantun sanadiyyar annobar corona, yana
mai cewa gwamnati ta bayar da damar bude makarantun islamiya da
tsangaya a jihar nan.
Ya Kara da cewa matukar ana son ganin warakar kowacce irin cuta
wajibi ne a koma ga Allah ta hanyar bai wa makarantun addini damar
ci gaba da ilimantar da yara da sanya su yin addu’o’i ga kasa.
Wakilin jaridar bustandaily ya Al ameen Ahmad ya rawaito cewa a yayin
Al’kunutun malamai daga sassan jihar Kano daban daban ne suka
halarta inda kuma suka gudanar da addu’o’i na musamman ga kasar
nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *