Mutane biyu sun mutu a yayin wata zanga-zanga a yau
1 min read
Rahotanni daga Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya sun rawaito cewa
mutum biyu sun mutu sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ‘yan
ƙungiyar IPOB masu son ɓallewa daga Najeriya da kuma ‘yan sanda.
Jaridu a ƙasar, sun ce lamarin ya faru ne ranar Lahadi kuma an jikkata
wasu dama daga cikin ‘ya’yan ƙungiyar da suka fito zanga-zanga.
Kazalika, jaridar The Nation ta ce an kama wasu da yawa daga cikinsu.
Wani da ya shaida lamarin ya faɗa wa jaridar Punch cewa mutum 10
aka kama.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Ahmad Abdurraham bai amsa saƙon
tes da Punch ta aika masa ba har zuwa lokacin wannan rahoton.