July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tawagar ECOWAS a Mali ta ziyarci Boubacar Keita

1 min read

Tawafar da ƙungiyar ECOWAS ta tura Mali ƙarƙashin jagorancin Tsohon
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta isa Mali, kwanaki kaɗan
bayan juyin mulkin da aka yi.
Tawagar dai ta tattauna da sabbin shugabannin sojojin ƙasar da suka
karɓe mulki, haka zalika sun samu tattaunawa da Tsohon Shugaban
ƙasar Ibrahim Boubacar Keita wanda aka hamɓarar da gwamnatinsa a
Talatar da ta wuce.
“Mun gan shi, lafiyarsa ƙalau, ” in ji Mista Jonathan, kamar yadda
kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Ya kuma ƙara da cewa tattaunawar da ake yi da sojojin domin kawo
sulhu na tafiya lami lafiya, ya ce “muna fatan komi zai tafi daidai”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *