July 16, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Har Yanzu Ana Fuskantar Mawuyacin Halin Rayuwa a Najeriya

2 min read

Yayin da ake ci gaba da neman hanyar magance annobar
Coronavirus, yanzu matsalar dake addabar jama’a
musamman talaka ita ce mawuyacin halin rayuwa, da suka
hada da rashin kudi da kuma tsadar rayuwa.
Kawo yanzu gwamnatin tarayyar
Najeriya da kuma jihohi na ikirarin kashe dubban
Miliyoyin Naira wajen tallafawa masu karamin karfi,
domin rage radadin wahalar rayuwa da ake fama da ita
sakamakon annobar Covid-19 da aka fi sani da
coronavirus.
Ahmad Tukur Jada, daya daga cikin shugabanin
kungiyoyin kananan manoma a Najeriya, ya bayyana
wa sashen Hausa irin kalubalen da talakawa ke
fuskanta a wannan lokaci na annoba, wanda ya hada
da tsadar rayuwa. Game da batun tallafin corona kuwa
ya ce babu abin da suka gani.
Sai dai yayin da talakawa ke kokawa, tuni wasu wakilai
da kuma kungiyoyi suka fara neman hanyar tallafawa,
domin ragewa al’umma wahalar da suke ciki.
Dan Majalisar Dokokin jihar Taraba, Bashir Muhammad
Bape, ya fadawa Muryar Amurka cewa a mazabarsa ta
Nguroje, sun sayi Babura guda 60 da injinan markade
da kuma Kekunan dinki suka rabawa al’umma domin
su sami hanyar gudanar da rayuwa.
Ya zuwa yanzu dai, an bude wasu kasuwanni a jihar
Taraba sai dai ana kokawa kan yadda wasu kayayyakin
more rayuwa irin su Hatsi da masu karamin karfe
matukar bukata na kara yin tashin gwauron zabi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *