June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kidayar shagunan siyar da magani a kano zai kawo karshen bata gari-DFID lafiya

2 min read

Kungiyar masu kananan shagunan siyar da magani reshen Jihar Kano, ta bukaci ‘yan kungiyar dasu bada hadin kai wajen kidayar shagunan da za’a fara gudanarwa a nan Kano.

Shugaban kungiyar Alhaji Muhammad Nura Abubakar ne,ya bayyana haka, a yayin taron wata kungiya mai suna DFID Lafiya ta shirya da hadin gwiwar kasar burtaniyya,Wanda aka yiwa lakabi da lafiya training workshop.

Alhaji Muhammad Nura ya kumaKara da cewa, wannan shiri da aka kawo jihar Kano zai kara tsaftace Sana’ar siyar da magani.

Alhaji Muhammad Nura ya kuma ce, akwai ci gaba mai alfanu ga duk masu rijista da kungiyar, kasanceawar Sana’ar sai da magani sana’a ce wacce ke da bukatar kulawa ta musamman.

Shugaban ya kuma godewa wannan kungiya bisa kawo wannan shiri jihar Kano.

A nasa jawabin Babban sakatare hukumar kula da asbitoci da gurin shan magani da wajen aski da kuma masu magungunan gargajiya masu zaman Kansu, Kano,Dakta Usman Tijjani Aliyu, cewa yayi wannan shiri za’a shiga lunguna da sako na jihar Kano domin tantance su,Wanda hakanne zai basu damar gudanar da kawo gyare-gyare a fannin.

Shima da yake nasa sakacin shugaban hukumar kula da ingancin magunguna ta kasa reshen Jihar Kano, Pharmacist Sulaiman Chiroma ya ce, wannan shiri zai kawo ci gaba bama a kano ba,harma kasa baki daya domin tabbatar da ingancin magunguna.

Haka zalika ya kuma ce hukumar na kokarin fitar da batagarin masu siyar da magunguna musamma masu siyar da magani da hukumar ta
haramta siyarwa.

A jawabin sa shugaban kungiyar DFID lafiya,Alhaji Dayyabu Muhammad Yusuf,ya ce jihoyi biyar ne zasu amfana da wannan shiri, Wanda kasar ta burtaniyya ta shirya, tallafawa masu kantunan maganin.

Ya kuma ce zasu gudanar da shirin a kananan hukumomi 44 dake fadin a jihar Kano baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *