June 23, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rashin zuwa makaranta ‘ya fi cutar korona illa ga dalibai – Whitty

2 min read

Ƙananan yara za su fi shiga haɗarin cutuwa a kan hanyarsu ta
komawa gida daga makaranta a wata mai zuwa fiye da illar da cutar
korona za ta yi musu idan suka kamu da ita, a cewar babban mai
bayar da shawara kan harkar lafiya a Birtaniya.
Farfesa Chris Whitty ya ce “yiwuwar mutuwar yara ta hanyar korona
ba wata mai yawa ba ce – amma rashin yi musu darasi “na ɓata
rayuwar yaro ta lokaci mai tsawo”.
Miliyoyin yara ne ake sa ran za su koma makaranta a Ingila da Wales
da Ireland ta Arewa a ‘yan makonni masu zuwa. Farfesa Whitty ya kuma bayyana cewa korona za ta ci gaba da zama
ƙarfen ƙafa a cikin wata tara masu zuwa.
Gwamnati ta ce ana sa ran dukkanin ɗalibai za su koma azuzuwansu
don ɗaukar cikakkun darusa nan da watan Satumba.
Bayanan nasa na zuwa ne yayin da shugaban da kuma mataimakinsa
ke cewa “babu wani zaɓi maras haɗari” sannan kuma yana da
muhimmanci iyaye su san amfani da kuma haɗarin sake buɗe
makarantu.
Wani ɗan majalisar ministocin Birtaniya ya ce za a buɗe makarantun
cikin ƙwarin gwiwa idan Sashen Ilimi ya bayar da cikakkun bayanai ga
iyaye da malamansu.
Saƙo ga iyaye
Farfesa Whitty ya yi amfani da tattaunawar tasa wurin shaida wa
iyaye akwai hujjoji da ke nuna cewa idan yara ba sa zuwa makaranta
sun fi shiga haɗarin kamuwa da “lalurar ƙwaƙwalwa da kuma ta
jikinsu a cikin lokaci”.
Ya ƙara da cewa akasarin yaran da suka mutu sakamkon korona
suna da wasu cutukan na daban “masu tsanani”.
Alƙaluma daga ofishin Hukumar Ƙididdiga na Birtaniya sun nuna
cewa an samu mutuwar mutum 10 saboda korona a tsakanin ‘yan
shekara 19 zuwa ƙasa a Ingila da yankin Wales tsakanin watan Maris
zuwa Yuni – an samu mutuwar 46,725 tsakanin ‘yan shekara 20 zuwa
sama.
Daga cikin yara ‘yan makaranta fiye da miliyan ɗaya da suka shiga
makarantun rainon yara da kuma firamare a Ingila a watan Yuni,
guda 70 da kuma ma’aikata 128 ne suka kamu da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *