‘Satar mutane na karuwa kan iyakokin Najeriya da Nijar’
2 min read
Al’umomin da ke zaune kan iyakokin Najeriya da Jamhuriyar Nijar
sun koka kan abin da suka kira karuwar satar jama’a a yankunan.
Jama’ar kananan hukumomin Gudu da Tangaza a jihar Sokoto da ke
Najeriya sun ce a kowacce rana sai an sace mutane a yankin lamarin
da ya sanya wasu tserewa zuwa jamhuriyyar Nijar.
Wani da ya bukaci a boye sunansa, ya shaida wa BBC cewa masu
satar mutanen na iya zuwa kowane lokaci su sace jama’a. “Sun zo kusa da wani gari kusa da Tangaza suka saci wani bawan
Allah tare da matarsa, hankalin kowa a tashe yake,” saboda a
cewarsa, babu tabbas na tsira a irin wannan lamarin.
Shima wani mutum ya fada wa BBC cewa masu satar mutanen suna
shiga cikin gari, ko da rana -“ni ga shi an dau dana, dan wana,” amma
ya ce sai da suka yi hadaka aka ba da kudi sannan aka saki dan da
aka yi garkuwa da su.
A cewarsa, masu satar mutanen a baya-bayan nan sun yi awon gaba
da wsu mutum uku a don haka ya ce matsalar satar mutanen karuwa
take yi.
Alhaji Bala Suleiman Giwa daya ne daga cikin wadanda suka tsere
zuwa Nijar kuma ya ce masu satar mutanen sun dauki matarsa
sannan bayan wata shida sun sace mahaifinsa.
Ya ce shi kansa baya tunanin zai tsira daga barazanar mutanen da ke
garkuwa da jama’a.
Sai dai rundunar ‘yan sanda a jihar Sokoto ta bakin kakinta ASP
Muhammad Abubakar Sadiq ta ce sun kaddamar da wata rundunar
hadin gwiwa don yaki da matsalar a sassan jihar.